logo

HAUSA

An Zabi Mutane 10 Da Za Su Zama ‘Yan Sama Jannati Na Kasar Sin Karo Na 4

2024-06-11 14:14:00 CMG Hausa

Hukumar kula da ayyukan kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta sanar a yau Talata cewa, an zabi mutane 10 da suka hada da matuka kumbo 8 da masu kula da gwaje-gwaje da kayayyakin aiki 2, domin aikin 'yan sama jannati na kasar Sin karo na 4.

A cewar hukumar, daya daga cikin masu gwaje-gwaje da gudanar da bincike dan asalin yankin musammam na Hong Kong ne, yayin da dayan kuma ya fito daga yankin musammam na Macao. (Fa’iza Mustapha)