logo

HAUSA

Sin ta tsara burikan rage hayakin Carbon a bangaren samar da siminti

2024-06-10 20:30:21 CMG Hausa

Hukumomin kasar Sin sun tsara jerin burikan da suke son cimma a masana’antar samar da siminti, a yunkurin kasar na komawa ga tsarin raya tattalin arziki ba tare da fitar da hayakin Carbon mai yawa ba.

Daga shekarar 2024 zuwa 2025, kasar Sin na shirin rage fitar da hayakin Carbon da kimanin ton miliyan 13 ta hanyar yi wa masana’antar siminti garambawul da sabonta kayayyakin aikin samar da simintin.

Wannan na kunshe ne cikin wani shirin aiki da sassan gwamnatocin kasar suka fitar, ciki har da hukumar raya kasa da aiwatar da gyare-gyare, wadda ke zaman hukumar koli mai tsara ayyukan raya tattalin arzikin kasar. (Fa’iza Mustapha)