logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Taraba ta ce za ta yi kokarin cike ka`idojin da suka kamata domin ta samu damar karbar tallafin kudi daga asusun UNICEF

2024-06-10 15:00:19 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da kudirin ta na biyan kason kudin da suka wajaba a kan ta don samun damar karbar tallafin dola miliyan uku da dubu dari 4 daga asusun UNICEF domin yakar matsalolin karancin abinci mai gina jiki a tsakanin kananan yara da mata masu juna biyu dake jihar.

Gwamnan jihar Mr Agbu Kefas ne ya tabbatar da hakan ta bakin mataimakin sa Alhaji Aminu Alkali a karshen makon jiya lokacin da yake karbar bakuncin wata tawagar asusun Unicef a fadar gwamnatin jihar dake garin jalingo, ya ce karancin abinci mai gina jiki yana daya daga cikin matsalolin da yanzu haka bangaren kiwon lafiyar jihar ke fuskanta.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kamar dai yadda yake kunshe cikin wani rahoto da asusun na UNICEF a Najeriya ya fitar, ya nuna cewa kusan kananan yara miliyan 1 da dubu dari 3 ne aka ceto daga matsalar rashin abinci mai gina jiki a 2023, kari a kan yara dubu dari 4 da aka yiwa magani sakamakon karancin nau`ikan abinci mai gina jiki a 2022.

Da yake jawabi ga tawagar asusun na Unicef mataimakin gwamnan jihar ta Taraba ya ce bisa rahotannin da ya samu daga ma`aikatar lafiyar jihar, ya nuna cewa yaro daya daga cikin yara hudu yana fama da matsalar karancin abinci mai gina ciki wanda haka ke haifar da rashin girman sa sosai.

Ya ce gwamnatin jihar ta Taraba za ta yi bakin kokarin ganin ta samu cin gajiya daga asusun kula da harkokin abinci mai gina jiki dake karkashin Unicef.

“Batun kudin tallafi da ake samu daga asusun, shi ne ginshiki wajen nasarrorin da gwamnatin jihar ke samu a kan sha`anin kiwon lafiya, amma an yi fatan cewa da zarar gwamnatin jihar ta bayar da kaso ta, asusun na Unicef zai hanzartar bayan da kudade domin fara daukar matakan gaggawa wajen dakile karuwar karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara dake jihar.”

A nasa bangaren babban jami`in asusun na UNICEF mai kura da ofishi dake Buachi Dr. Tusha Rane yace a shirye asusun yake ya yi aiki tare da gwamantin jihar Taraba wajen tabbatar da samar da dukkan tallafin da ake bukata domin raba su ga yankunan kananan hukumomi 16 dake jihar.(Garba Abdullahi Bagwai)