logo

HAUSA

Faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da tawagar gungun bankin duniya

2024-06-08 16:40:14 CMG Hausa

Faraministan Nijar kuma ministan kudi, Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana a ranar jiya 7 ga wannan wata da muke ciki a fadarsa da ke birnin Yamai da wata tawagar gungun bankin duniya da ke karkashin wakilin bankin duniya da ke Nijar Han Freaters tare da rakiyar babban manajan kudin kasa da kasa game da yankin Sahel na AES da suka hada da Nijar, Burkina Faso, Chadi da Mali, mista Sylvain Kakou.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Bayan fitowarsa daga wannan ganawa, wakilin gungun bankin duniya Han Freaters ya jaddada cewa musanyar da suka yi tare da faraminista ta mai da hankali kan tawagar hadin gwiwa ta kasa da kasa kan harkokin kudi IFC da bankin duniya. Mun zo nan domin tattauna hanyoyin karfafa bangaren masu zaman kansu da kudi na kasar Nijar da suka galabaita sosai dalilin takunkumi da wasu matsaloli a wadannan watanni na baya bayan nan. Mun zo tare da kwararru domin kimanta matsalar da tantance yadda bankin duniya zai taimakawa kasar da hukumominta na su karfafa wadannan bangarori, inji mista Han Freaters.

A nasa bangare, mista Sylvain Kakou, babban manajan kudin kasa da kasa domin kasashen Burkina Faso, Chadi, Nijar da Mali, ya nuna cewa ci gaban bangaren masu zaman kansu, ya kasance abin maida hankali na farko ga gwamnatin Nijar, domin karfafa karfin masana’antun kasa da kuma matasa masu kamfanoni.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.