logo

HAUSA

Shugabar ICRC: Aikin jin kai mataki ne na farko da ake bukata don shimfida zaman lafiya

2024-06-08 16:41:51 CMG Hausa

A kwanakin baya, shugabar kwamitin Red Cross na duniya wato ICRC Mirjana Spoljaric Egger ta bayyanawa wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin CMG cewa, ana bukatar shekaru da dama na yin kokarin samun farfadowa daga rikici, gidaje da dama sun lalace, an raba iyalai da juna, abu ne mai wuya a tinkari irin wannan mawuyacin hali. Shugabar ta yi kira ga kasa da kasa da su yiwa juna kashedi, wato hanya daya tilo wajen samun zaman lafiya ita ce bin ka’idojin yake-yake, da tabbatar da yin mu’amala da juna, da yin aikin jin kai a kowane lokaci, da kin amincewa da ayyuka masu sabawa ra’ayin jin kai, ta hakan za a mayar da odar siyasa yadda ya kamata. Hanya mafi kyau wajen daidaita matsalolin jin kai ita ce yin shawarwari ta hanyar siyasa, ya kamata a ba da jagoranci ta hanyar siyasa, da kawo karshen rikici, da maido da zaman lafiya, amma bai kamata a yi amfani da karfin soja ba.

Game da rawar da kasar Sin ta taka kan sha’anin jin kai da tabbatar da dokokin jin kai na duniya a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, Spoljaric ta bayyana cewa, Sin ta shiga harkokin duniya da yankuna a matsayin bangare mai muhimmanci a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kiyaye tsaro da zaman lafiya. Don haka, tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa a wannan fanni don sa kaimi ga kasa da kasa da su girmama dokokin jin kai na kasa da kasa. (Zainab Zhang)