logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin inganta muhallin teku

2024-06-08 16:10:35 CMG Hausa

Kasar Sin ta kara kaimi wajen gina kyawawan mashigin teku, a kokarinta na kiyaye yanayin muhallin teku.

Ma’aikatar kula da yanayin muhalli ta kasar Sin ta fitar da wani shiri na gina mashigin teku sama da 110 a fadin kasar nan da shekarar 2027, wadanda za su taimaka wajen samun jituwa tsakanin mutane da muhallin teku. Ma’aikatar ta bayyana cewa, za a iya ganin “tsaftataccen ruwan teku da tsaftataccen rairayin bakin teku, da garken kifaye, da na tsuntsayen teku” a lokaci guda.

Adadin 110 zai kai kusan kashi 40 cikin 100 na manyan mashigin teku a kasar Sin, a cewar ma'aikatar.

Har ila yau, shirin ya tsara manufar mayar da birane bakwai, ciki har da Xiamen, zuwa yankunan gwaji, inda za a ware dukkan yankunan bakin teku a matsayin kyawawan mashigin teku.

Shirin ya ba da cikakken bayani game da ayyuka guda uku, wadanda suka hada da karewa da maido da ainihin yanayin muhallin teku, da kyautata muhimman hanyoyin fitar da guabataccen ruwa cikin teku. (Yahaya)