logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci taron ministocin waje na kasashen BRICS

2024-06-07 16:29:29 CMG Hausa

A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mao Ning ta sanar da cewa, bisa goron gayyatar da aka ba shi, mamban ofishin harkokin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin waje na kasar, zai je birnin Nizhni Novgorod na kasar Rasha, don halartar taron ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS. (Lubabatu Lei)