logo

HAUSA

Sin za ta inganta matakan tunkarar barkewar cututtuka masu yaduwa

2024-06-06 10:44:56 CMG Hausa

Hukumomin lafiya na kasar Sin, sun gabatar da sabbin matakan tabbatar da karfafa aikin tunkarar barkewar cututtuka masu yaduwa.

Bisa wani yunkuri na hadin gwiwa tsakanin hukumar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka da hukumar lafiya ta kasar Sin, matakan sun bayyana cewa, tawagogin kai agajin gaggawa domin dakilewa da kandagarkin cututtuka masu yaduwa, za su kunshi tawagar kwararru da cibiyoyin kandagarkin yaduwar cututtuka na tafi da gidanka.

Wadannan tawagogi sun kunshi ma’aikatan agaji na gaggawa da kwararrun jami’ai da kuma ma’aikatan kula da hidimomi da jigilar kayayyaki.

Matakan sun kuma bayyana cewa, kwararrun jami’an na nufin kwararru a bangarorin da suka shafi nazarin yanayin yaduwar cututtuka tsakanin mutane da na gwaje-gwaje da bayar da jinya da fasahar sadarwa da nazarin halayyar dan adam.

Haka zalika sun bayyana cewa, akwai bukatar karfafa ayarin masu kai daukin gaggawa, tun daga matakin kasa zuwa na larduna, domin inganta baki dayan karfin kasar na tunkara da dakile barkewar cututtuka masu yaduwa. (Fa’iza Mustapha)