logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na Venezuela

2024-06-05 20:20:41 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Venezuela Yvan Gil Pinto a yau Laraba a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Wang Yi ya ce, a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Venezuela, kamata ya yi bangarorin biyu su kiyaye muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a matsayin jagora, da takaita nasarorin da aka samu cikin shekaru 50 da suka gabata na dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen 2, da fito da manyan tsare-tsare bisa hangen nesa, da sanya sabbin ma’ana cikin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.

Yvan Gil Pinto ya ce, Venezuela a ko yaushe tana mutunta ka'idar Sin daya tak a duniya, kuma tana godiya sosai ga kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa wajen raya zamantakewa da rayuwar jama'ar Venezuela. (Yahaya)