logo

HAUSA

MOFA: Batun Taiwan ba ya bukatar tsangwama daga waje

2024-06-05 20:09:10 CMG Hausa

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fada a wata hira da ya yi cewa, idan aka samu rikici na soji tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan, bai kawar da yiwuwar shiga tsakani na sojojin Amurka ba. Dangane da hakan, yayin da take mayar da martani, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau 5 ga wata cewa, Taiwan wani yanki ne da ba zai taba rabuwa da kasar Sin ba, kuma batun Taiwan lamari ne na cikin gida na kasar Sin wanda ba ya lamuntar tsoma baki daga waje.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong zai jagoranci wata tawaga da za ta halarci taron manyan jami’an ASEAN da Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da taron manyan jami’ai na gabashin Asiya, da taron manyan jami’ai na dandalin tattaunawar ASEAN da za a yi a Vientiane a ranar 7 zuwa 8 ga wata. Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin na fatan yin mu'amala mai zurfi tare da dukkan bangarorin da za su halarci tarukan, domin sa kaimi ga samun sabbin ci gaba a hadin gwiwar dake tsakanin kasashen gabashin Asiya, da ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaba tare.

Ban da haka kuma, kasar Sin ta taya firaministan kasar Indiya Narendra Modi murnar samun nasara a zaben kasar, a cewar Mao Ning. Ta kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Indiya wajen ci gaba da tabbatar da moriyar kasashen biyu da al'ummominsu, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar huldar dake tsakanin kasashen biyu bisa turba mai inganci da kwanciyar hankali.

Kasar Sin ta kuduri aniyar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsibirin Koriya, kuma tana adawa da duk wata magana ko aiki da ke kara ta'azzara rikici a tsibirin, a cewar Mao Ning biyo bayan shawarar da kasar Koriya ta Kudu ta yanke ta dakatar da yarjejeniyar soja da kasar Koriya ta Arewa da ita suka daddale a ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2018. (Yahaya)