Kumbon Sin ya tashi daga bangaren duniyar wata mai nisa dauke samfura
2024-06-04 10:41:58 CMG Hausa
Na’urar tashi ta kumbon binciken duniyar wata ta kasar Sin wato Chang’e-6, ta tashi daga doron duniyar wata da safiyar yau Talata, dauke da samfuran da ta tattaro daga yanki mai nisa na duniyar watan, lamarin da ya kasance wani gagarumin nasara a tarihin dan adam na binciken duniyar wata.
Hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta ce na’urar ta shiga falakin da aka tsara a zagayen wata.
An harba kumbon Change’e-6 da ya kunshi na’urorin zagaye da ta sauka da tashi da ta dawowa, kamar magabacinsa Chang’e-5, a ranar 3 ga watan Mayu. A kuma ranar 2 ga wata ne na’urar tashi da sauka ta kumbon, ta sauka a yankin gulbin dake kudancin duniyar wata da ake kira South Pole-Aitken Basin.
Kumbon Change’6 ya kammala ayyukansa masu fasaha da tattara samfura, kuma kamar yadda aka tsara, samfuran na cikin wani mazubi dake cikin na’urar tashi dake jikinsa. (Fa’iza Mustapha)