Xi Jinping ya mika sakon murna ga sabuwar shugabar Iceland
2024-06-04 20:25:01 CMG Hausa
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga Halla Tomasdottir da zama sabuwar shugabar kasar Iceland.
A cikin sakon, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekarun baya-bayan nan, an raya huldar dake tsakanin Sin da Iceland yadda ya kamata. An samu ci gaba kan hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli ta hanyar amfani da makamashin zafin karkashin kasa, da al’adu, da yawon shakatawa da sauransu. Sin ta dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakaninta da Iceland. Xi ya ce, a shirye yake ya kokarta tare da shugaba Tomasdottir wajen zurfafa amincin kasashen biyu a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwarsu don raya huldar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab Zhang)