logo

HAUSA

Wang Yi: Karin kasashe na nuna goyon baya, za a kyautata fatan samun zaman lafiya

2024-06-04 21:32:10 CMG Hausa

A ranar 4 ga wata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Türkiye Hakan Fiddan suka gana da manema labarai tare a nan birnin Beijing, inda suka yi karin haske kan muhimmin matsayin kasar Sin game da warware rikicin Ukraine.

Wang Yi ya ce, game da batun Ukraine, matsayin kasar Sin shi ne sa kaimi ga yin shawarwarin zaman lafiya, ba tare da tangarda ba, kuma akai akai. A baya-bayan nan kasashen Sin da Brazil sun fitar da takardar mai kunshe da fannoni 6 da suka cimma daidaito a kai, dangane da kara azama kan warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. A cikin mako guda kacal, kasashe 45 daga nahiyoyi 5 sun mayar da martani mai kyau kan takardar ta hanyoyi daban daban, inda wasu 26 suka tabbatar da amincewarsu ko kuma suna nazari sosai kan amincewa. Rasha da Ukraine su ma sun amince da mafi yawan abubuwan da aka tanada cikin takardar. Wannan ya sake nuna cewa, takardar ta dace da abin da akasarin kasashe ke fata. Kasar Sin ta yi imanin cewa, yayin da aka samu karin kasashen da ke goyon bayan takardar, za a kara kusantar ranar gudanar da taron zaman lafiya na gaskiya, kuma za a kara kyautata fatan samun zaman lafiya. (Yahaya)