logo

HAUSA

Shen Yiqin ta jaddada muhimmancin tabbatar da kiwon lafiya da walwalar yara

2024-06-01 17:23:20 CMG Hausa

Mambar majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, ta jaddada muhimmancin kara zage damtse wajen kula da yara, da tabbatar da sun girma cikin koshin lafiya da walwala.

Shen, wadda kuma ita ce shugabar kwamitin kasa mai lura da harkokin yara da mata, karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, ta yi tsokacin ne yayin da ta halarci cibiyar lura da kananan yara ta kasar Sin, albarkacin ranar yara ta duniya da aka yi bikin ta a ranar Asabar.

Yayin da take cudanya da yara a cibiyar, Shen ta ja hankalin su da su kuduri aniyar cimma manyan burika, kana su yi kokarin samun ci gaba a dukkanin fannoni.

Har ila yau, jami’ar ta yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai, da su aiwatar da shirin kasa na bunkasa harkokin yara, da baiwa ayyuka masu nasaba da hakan cikakken muhimmancin da ya dace. (Saminu Alhassan)