Sin ta cimma nasarar harba jerin taurarin dan Adam 5
2024-05-31 15:29:10 CMG Hausa
Da misalin karfe 7:39 na safiyar yau Juma’a, kasar Sin ta cimma nasarar harba jerin tauraron Bil Adam 5 da aka yi wa lakabi da Aurora Constellation, ta hanyar amfani da roka mai daukar kayayyaki samfurin Ceres-1, daga birnin Jiuquan na kasar Sin. Kuma tuni taurarin suka shiga falakinsu.
Wannan shi ne karo na 13 da aka yi amfani da rokar Ceres-1 wajen gudanar da wannan aiki. (Amina Xu)