logo

HAUSA

Yawan wutar lantarki da jerin madatsun ruwa dake Sin suka samar a rubu’in farko na bana ya zarce kilowatts biliyan 52

2024-05-31 14:01:43 CMG Hausa

Bisa labarin da kamfanin Sanxia na kasar Sin ya bayar, an ce, yawan wutar lantarki da jerin masu samar da makamashi mai tsabta mafi girma a duniya dake Sin suka samar a rubu’in farko na bana ya zarce kilowatts biliyan 52, hakan ya samar da cikakken makamashi wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba.

Jerin madatsun ruwa da suka hada da na Wudongde, da Baihetan, da Xiluodu, da Xiangjiaba, da Sanxia, da Gezhouba na kasar Sin, wadanda suka kasance jerin masu samar da makamashi mai tsabta mafi girma a duniya, sun samar da wutar lantarki fiye da kilowatts biliyan 52 a rubu’in farko na bana, kwatankwacin tsimin kwal ton miliyan 15, wanda kuma ke iya biyan bukatun amfani da wutar lantarki na mutane miliyan 54 a shekara daya. (Zainab Zhang)