logo

HAUSA

Xi Jinping ya tattauna da sarkin kasar Bahrain

2024-05-31 20:44:14 CMG Hausa

A yammacin yau Jumma’a ranar 31 ga watan Mayu a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya tattauna da sarkin Bahrain Sheikh Hamad Bin Isa al-Khalifa, wanda har yanzu ke ziyarar aiki kasar ta Sin, tare kuma da halartar bikin bude taron minisroci karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa.

A yayin ganawar, shugabannin kasashen biyu sun sanar da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni ta Sin da Bahrain.

Bayan tattaunawar kuma, shugabannin biyu sun ganewa idanunsu yadda aka rattaba hannu kan wasu takardun hadin kai da dama da suka shafi fannonin zuba jari, rage gurbata iska, kasuwanci ta yanar gizo, tattalin arzikin dijital, da dai sauransu.

Kafin haka kuma, shugaba Xi ya shirya wani biki a wajen babban dakin taron al’ummar, don maraba da zuwan sarki Hamad, kana a daren ranar, ya shirya masa liyafa a wurin.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)