Firaministan Pakistan zai kawo ziyara kasar Sin
2024-05-31 18:59:22 CMG Hausa
Bisa gayyatar da firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi masa, firaministan kasar Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuni.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ce ta bayyana hakan a yau Juma’a.