logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya soke takunkuman da ya kakkaba da ba su dace da halin da ake ciki a yanzu ba

2024-05-31 14:52:31 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce Sin na kira ga kwamitin sulhu na majalisar ya daidaita takunkuman da ya kakkabawa Sudan ta Kudu bisa takatsantsan, kuma tana fatan kwamitin zai mayar da hankali kan kiran da kasashen Afirka suke yi masa da  muhimman batutuwan da Afrika ke dora muhimmanci a kai, don daidaitawa da soke wasu takunkuman da ya kakkabawa kasar.

Geng Shuang ya bayyana haka ne cikin jawabin bayani da ya gabatar bayan kwamitin sulhun ya kada kuri’a kan daftarin kudurin sanya wa Sudan ta Kudu takunkumi.

A cewarsa, Sin ta janye jiki daga kada kuri’ar. Yana mai cewa, a halin yanzu, gwamnatin kasar na bukatar tallafi da taimako a maimakon takunkumi da matsin lamba. Ya ce cikin shekaru 20 da suka gabata, tsarin kakkaba takunkumi na kwamitin ya rika habaka, amma an yi biris da bukatu masu dacewa, na wasu kasashen Afrika na sassautawa ko soke takunkuman da aka sanya musu. (Amina Xu)