logo

HAUSA

Xi Jinping: Sin na fatan kafa tsare-tsaren hadin kai biyar tsakaninta da kasashen Larabawa

2024-05-30 13:25:11 CMG Hausa

 

Da safiyar yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashen Larabawa a nan birnin Beijing, tare da gabatar da jawabi.

Xi Jinping ya nuna cewa, an cimma nasarar tabbatar da ayyuka 8 na hadin kansu da ya gabatar a yayin taron koli na kasashen Sin da Larabawa karo na farko. Kuma Sin na fatan bisa wannan harsashi mai kyau, za a inganta hadin kan bangarorin biyu wajen kafa wasu karin tsare-tsaren hadin kai biyar, ta yadda za su gaggauta aikin kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya. Wato da farko dai, tsarin gaggauta aikin kirkire-kirkire mai kuzari. Na biyu tsarin zuba jari mai girma. Na uku, tsarin hadin kai ta fuskar makamashi a mabambanta bangarori. Na hudu kuma, tsarin tattalin arziki da ciniki na moriyar juna da daidaito. Na karshe shi ne, tsarin mu’ammalar al’adu na bambanta bangarori.

Kazalika, Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin na fatan mai da huldar Sin da kasashen Larabawa matsayin wani misali ga duniya wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa da kasa. Ya kara da cewa, Sin na nacewa ga manufar “Kafa kasashen Palasdinu da Isra’ila”, kuma tana goyon bayan Palasdinu ta zama mambar MDD, da kuma kiran taron kasa da kasa mafi girma dake da cikakken iko da daukar matakan a zo a gani.

Dadin dadawa, Xi Jinping ya ce, Sin za ta kira taron koli karo na 2 tsakanin Sin da kasashen Larabawa a shekarar 2026. (Amina Xu)