logo

HAUSA

Hakkin bil Adam iri na Amurka matakin gatanci da babakere ne

2024-05-30 13:30:07 CMG Hausa

 

Hukumar gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoton yanayin keta hakkin Bil Adama da ake ciki a kasar Amurka a shekarar 2023, inda ta ruwaito sahihan misalai da dama, ta yadda duk duniya za su iya gano hakikanin halin da Amurka ke ciki wajen keta hakkin Bil Adam.

A cewar rahoton, a bangaren hare-haren bindiga, bisa kididdigar da shafin yanar gizo mai bayani kan hare-haren bindiga na Amurka ya bayar, an ce, a shekarar bara, yawan hare-haren bindiga da ya auku a Amurka ya kai a kalla sau 654, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin dubu 43, wato kwatankwacin mutuwar mutane 117 a kowace rana. Rahoton ya kuma bayyana cewa, ’yan siyasar Amurka suna yunkurin cimma burinsu na kashin kai da suka hada da na kudi da siyasa, inda suka gaza kai wa ga matsaya daya kan kayyade yawan bindigar da ake mallaka, lamarin dake kawo mummunar illa ga fararen hula kawai.

Za a iya fahimta cewa, hakkin bil Adama irin na Amurka matakin gatanci ne ga wasu, kana ya kasance hujjar da ’yan siyasa suke fakewa da ita wajen aiwatar da babakere. Bisa la’akari da wadannan abubuwan, hakkin bil Adama da ’yan siyasar Amurka suke shelar karewa, abin dariya ne, ya kamata su yankewa kansu hukunci kan wannan batu. (Amina Xu)