Shugaba Xi ya yi kira da a zamanantar da ayyukan tsaron al’umma
2024-05-29 21:13:58 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga rundunar ‘yan sandan kasar, da ta ingiza matakan zamanantar da ayyukan tsaron al’umma. Xi, ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin da yake tsokaci a taron da ya yi da jami’an ‘yan sanda, mahalarta taron tsaron al’umma da ya gudana a birnin Beijing.
Kafin taron na bana, an gudanar da makamancinsa a shekarar 2019. Tun kuma wancan lokaci zuwa yanzu, an gudanar da manyan sauye sauye a tsarin gudanar da ayyukan tsaron al’umma, an kyautata kwazon ‘yan sanda na magance ayyukan gungun miyagun masu aikata laifuka, da laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo, da dai sauran su, lamarin da ya taimakawa kasar Sin ta zamo cikin jerin kasashe mafiya tsaro a duniya.
A shekarar 2023 da ta gabata, mizanin amincewar jama’ar kasar Sin da yanayin tsaron kasa, ya kai kaso 98.2 bisa dari, sabanin kaso 87.55 bisa dari a shekarar 2012. (Saminu Alhassan)