logo

HAUSA

Kongo Kinshasa ta sanar da sunayen jami’an sabuwar gwamnati

2024-05-29 14:45:31 CMG Hausa

 

Da sanyin safiyar Larabar nan, mai magana da yawun shugaban kasar Kongo Kinshasa, ya karanta jeren sunayen jami’an sabuwar gwamnatin kasar ta kafar gidan talibijin din kasar.

Jami’in ya ce firaministan kasar Judith Tuluka Suminwa ta gabatar da takardar sunayen, wadda ta samu amincewa daga shugaban kasar Félix-Antoine Tshisekedi.

Baya ga firaministan, sabuwar gwamnati na da mataimakan firaminista 6, da manyan ministoci 10, da kananan ministoci 24, da wakilai masu matsayin minista guda 4, da ma mataimakan minista 10. A sa’i daya kuma, an yiwa wasu hukumomin gwamnatin kasar kwaskwarima. (Amina Xu)