logo

HAUSA

Kasar Sin na nuna damuwa sosai kan matakin soja da Isra’ila ke aiwatarwa a birnin Rafah

2024-05-29 21:48:34 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba 29 ga wata cewa, kasarta na matukar damuwa kan matakin soja da Isra’ila ke kaddamarwa a birnin Rafah na zirin Gaza, inda da kakkausar murya ta yi kira ga Isra’ila, da ta saurari muryoyin sassan kasa da kasa masu rinjaye, ta dakatar da kai wa Rafah hari. (Murtala Zhang)