logo

HAUSA

Sin da Amurka sun gudanar da shawarwari a karo na biyu game da harkokin teku

2024-05-28 10:56:10 CMG Hausa

 

Wakilan bangarorin Sin da Amurka, sun gudanar da shawarwari karo na biyu kan harkokin teku ta kafar bidiyo a ranar 24 ga watan nan, inda jami’an bangarorin biyu suka yi musanyar ra’ayi kan yanayin da ake ciki a teku, da wasu batutuwan dake shafar sararin teku, kana sun kai ga cimma matsaya daya ta ci gaba da tuntubar juna, da kauracewa rashin fahimta, da yanke shawara bisa kuskure, da ma matakan dakile hadarorin da ake iya fuskanta a teku.

A bangarenta Sin ta bayyana rashin jin dadi game da matakin takara da Amurka ke dauka a yankunan sararin teku dake kewayen Sin, ta kuma kalubalanci Amurka da ta daina tsoma baki cikin sabaninta da sauran kasashe makwabtanta ta teku, kana ta kauracewa keta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Kaza lika, Sin ta jaddda cewa, ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, tushen siyasa ne na huldar kasashen biyu, kuma tushen tuntubar bangarorin biyu kan harkokin teku. (Amina Xu)