An yi watsi da shawarar baiwa Taiwan damar halartar taron WHA
2024-05-28 13:50:13 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi tsokaci game da yadda babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHA karo na 77, ya yi watsi da shawarar da wasu kasashe suka gabatar ta baiwa yankin Taiwan damar halartar taron a matsayin mai sa ido.
Da yake tsokaci game da lamarin a jiya Litinin, kakakin ya ce, hakan ya nuna a fili cewa, duniya na tare da manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma alkiblar tarihi ta karkata ga manufar, wadda ba zai yiwu a kalubalance ta ba. (Saminu Alhassan)