logo

HAUSA

An bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu

2024-05-28 10:56:23 CMG Hausa

A shekarar 1999, shugabannin kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu sun fara yunkurin hadin gwiwa tsakanin kasashen uku, a yayin da suka halarci taron shugabannin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ta ASEAN, da na kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu. Ya zuwa yanzu, shekaru 25 ke nan, kuma cikin wadannan shekarun da suka gabata, hadin gwiwa tsakanin kasashen uku ta bunkasa cikin yanayin sauye-sauye, ta kuma ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin yankin, da ma kasashen duniya baki daya, ta kuma ba da jagoranci ga dunkulewar yankin baki daya.

A ranar 27 ga watan nan da muke ciki, an yi taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu karo na 9 a birnin Seoul, fadar mulkin kasar Koriya ta Kudu. Bangarorin uku sun gabatar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka cimma matsayi daya kan aiwatar da “shirin hadin gwiwar kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu cikin shekaru 10 masu zuwa”, kuma aka zartar da shirin a yayin taro karo na 8, inda ya mai da hankali ga inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen uku, har a kai ga samun wani cikakken tsari mai amfani, domin kare zaman lafiya da karko na kasashen duniya, yayin da ake neman bunkasuwa da wadatar al’umma.

Manazarta na ganin cewa, a halin yanzu, ana fuskantar yanayin sauye-sauye a kasashen duniya, an kuma kasa samun farfadowar tattalin arziki kamar yadda ake fata. Taron ganawar shugabannin kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu na wannan karo, ya nuna kyakkyawan fatan kasashen uku, ta fuskar habaka hadin gwiwarsu, da kuma daidaito tsakanin kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kan manufofinsu masu nasaba da kasar Sin, da sassauta yanayin siyasa a tsakanin kasashen uku. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)