Tsawon hanyoyin mota da Sin ta shimfida a kauyuka ya karu da kashi 18.5% a cikin shekaru 10 da suka gabata
2024-05-28 11:01:02 CMG Hausa
Yau Talata, ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar da kididdiga dake cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, aikin shimfida hanyoyin mota da Sin ta gudanar a kauyukanta ya samu ci gaba mai armashi. Inda yawan kudaden da aka zuba ya kai kimanin dalar miliyan 58, kana tsawon sabbin hanyoyin da aka shimfida da kuma kyautata ya kai kilomita miliyan 2.5.
Tsawon hanyoyin dake sassan kauyukan kasar ya karu daga fiye da kilomita miliyan 3.88 a shekarar 2014 zuwa kilomita miliyan 4.6 a karshen shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 18.5%. (Amina Xu)