logo

HAUSA

‘yan sama jannatin Shenzhou-18 sun kammala aiki na farko a wajen tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin

2024-05-28 21:13:53 CMG Hausa

Tawagar ‘yan sama jannati na Shenzhou-18 dake cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta kammala aikinta na farko a wajen tashar a yau Talata.

Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin, ta ce yayin zagayen da suka yi na tsawon sa’o’i 8.5 a wajen tashar, ‘yan sama jannati da suka hada da Ye Guangfu da Li Cong da Li Guangsu, sun hada kai wajen gudanar da ayyukan da suka hada da sanya na’urorin kare tashar binciken daga tarkacen sararin samaniya da duba kayayyaki da na’urorin dake a wajen tashar, inda suka kammala da misalin karfe 6:58 na yammacin yau Talata, agogon birnin Beijing.

Tawagar za ta ci gaba da gudanar da tarin gwaje-gwajen kimiyya da zagaye a sararin samaniya da sarrafa na’urorin gudanar da ayyukan bincike. Wannan aiki ya nuna wani karin nasara a kokarin Sin na binciken sararin samaniya, haka kuma ya nuna yadda kasar ke kara karfi da kwarewa wajen gudanar da ayyukan sama jannati. (Fa’iza Mustapha)