logo

HAUSA

Liqiang ya gana da Kishida Fumio

2024-05-27 11:39:52 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da takwaransa na kasar Japan Kishida Fumio a daren jiya Lahadi, yayin da ya halarci taron shugabannin Sin da Japan da Koriya ta kudu, karo na 9 da aka gudanar a Seoul, fadar mulkin kasar Koriya ta kudu.

Yayin zantawarsu Li Qiang ya nuna cewa, a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco, shugaban kasar Sin Xi Jinping da Kishida Fumio, sun gana da juna, tare da cimma muhimmin matsayi guda, inda suka sake tabbatar da burinsu na gaggauta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni, lamarin da zai baiwa bunkasuwar huldarsu mai muhimmin jagoranci a siyasance. Ya ce Japan na fatan yin hadin kai da kasar Sin a karin bangarori, da tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ma inganta amincewa da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu, da ma daidaita bambancin ra’ayi dake tsakaninsu, kana da kokarin kafa huldar kasashen biyu mai ci gaban a zo a gani, kuma mai dorewa, wadda ke dacewa da bukatun sabon zamanin da muke ciki.

Batun dake shafar tarihi, da yankin Taiwan, su ne ke kasancewa ka’idojin tushen siyasa na huldar kasashen biyu, kuma batutuwa na tushe, na kare mutuncin kasar. Ya ce batun yankin Taiwan muhimmin abu ne na tushen muradun kasar Sin, kuma wani jan-layi da ba za a iya ketarewa ba. Sin na fatan Japan za ta nace ga alkawarinta, don samar da yanayi mai kyau ga kyautatuwar huldar kasashen biyu.

A nasa bangare, Kishida Fumio ya ce, bunkasuwar huldar kasashen biyu mai yakini, ba ma kawai za ta haifar da gajiya ga kasashen biyu kawai ba, har ma za ta amfani dukkanin fadin duniya. Ya ce Japan na nacewa ga matsaya da ta cimma, karkashin hadaddiyar sanarwar da kasashen biyu suka gabatar a shekarar 1972, ba tare da sauyawa ba ko kadan. (Amina Xu)