logo

HAUSA

An yi kira da a yi kokarin cimma burin Kafa kungiyar AU yayin bikin Ranar Afrika ta bana

2024-05-26 17:20:39 CMG Hausa

An gudanar da bikin Ranar Afrika a jiya Asabar, inda aka yi kira da a yi kokarin cimma burin kafa kungiyar Tarayyar Afrika (AU).

A kan gudanar da bikin wannan rana ne a duk ranar 25 ga watan Mayu, domin jinjinawa nasarorin da kungiyar hadin kan Afrika ta OAU ta cimma, wadda aka kafa a ranar 25 ga watan Mayun 1963, kafin a sauya sunanta zuwa Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta samu.

A sakonsa domin ranar, shugaban hukumar kula da ayyukan AU, Moussa Faki Mahamat, ya ce tun bayan kafuwar OAU, nahiyar ta 'yantar da kanta daga mulkin mallaka da mulkin fararen fata 'yan tsirarru. Haka kuma an raya tare da bunkasawa da baza komar albarkatunta na fasahohi da kimiyya da al'adu.

Ya ce Ranar ta Afrika, wata dama ce ta waiwaye domin duba nasarorin da aka samu da kuma nazarin hanyar da za a bi a nan gaba.

Da take bayyana matasa a matsayin wadanda suka mamaye sama da kaso 60 na al'ummar nahiyar, tarayyar AU mai kasashe mambobi 55, ta yi kira da a yi kokarin ganin an cimma halaltattun burikan dunkulewar nahiyar da samun ci gaba da zaman lafiya na bai daya, kamar yadda yake kunshe cikin ajandar raya nahiyar ta shekaru 50 da ake son cimmawa zuwa shekarar 2063. (Fa’iza Mustapha)