logo

HAUSA

Zirga zirgar jiragen kasa na dakon hajoji tsakanin Sin da Turai ta haura 90,000

2024-05-25 15:26:26 CMG Hausa

Da safiyar yau Asabar wani jirgin kasa na dakon kayayyaki, ya bar birnin Xi'an fadar mulkin lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin, inda ya nufi birnin Malaszewicze na kasar Poland. Tashin wannan jirgin kasa daga Sin zuwa Turai ya kafa wani sabon matsayi na zirga zirgar jiragen kasa tsakanin sassan biyu da adadin da ya zarce 90,000.

A cewar kamfanin lura da zirga zirgar jiragen kasa na kasar Sin, ya zuwa yanzu, jiragen kasa na dakon hajoji tsakanin Sin da Turai, sun yi dakon matsakaitan kwantenonin daukar kayayyaki sama da miliyan 8.7, wadanda darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 380.

Kaza lika, kamfanin ya ce tsakanin shekarar 2016 zuwa 2023 a duk shekara, adadin zirga zirgar jiragen kasa na dakon kayayyaki tsakanin Sin da Turai sun karu, daga 1,702 zuwa sama da 17,000. Har ila yau, darajar hajojin da aka yi dakon su ta wannan hidima sun karu daga dala biliyan 8 a shekarar 2016 zuwa dala biliyan 56.7 a shekarar 2023. (Saminu Alhassan)