logo

HAUSA

Rundunar ‘yan sandan tekun kasar Sin ta yi atisaye a gabashin tsibirin Taiwan

2024-05-24 15:37:43 CMG Hausa

Kakakin rundunar ‘yan sandan teku ta kasar Sin(CCG) Gan Yu, ya bayyana cewa, a yau Jumma’a, ayarin jiragen ruwa mai lamba 2304 na rundunar, ya yi atisayen ayyukan tabbatar doka a yankin tekun dake gabashin tsibirin Taiwan. A cewarsa, ayarin ya mai da hankali kan atisayen binciken takardun shaidu, da yin gargadi da korar jiragen ruwa da dai sauransu, a kokarin kimanta kwarewarsu ta gudanar da aikin sintiri da ma aikin gaggawa. (Maryam)