logo

HAUSA

Xi: Rubuta sabon babin zamanantarwa irin na Sin a Shandong ta hanyar zurfafa yin gyare-gyare

2024-05-24 19:57:59 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja, Xi Jinping, ya jadadda yayin da ya kai ziyara lardin Shandong cewa, ya kamata lardin Shandong ya sauke nauyin dake kansa yayin bunkasa kasar, ya aiwawar da sabon ra’ayin samun ci gaba a fannoni daban daban, da ci gaba da taka rawa wajen kafa sabon tsarin raya kasa, da karfafa karfin kirkire-kirkire kan bunkasuwar zamantakewar al’umma da tattalin arziki, da daga matsayin bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da kokarin rubuta wani sabon babi na zamanantarwa irin na Sin a lardin Shandong. (Safiyah Ma)