logo

HAUSA

Sin na maraba da kamfanoni daga ko ina domin su zuba jari tare da bunkasa kasar

2024-05-23 19:17:11 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin He Yadong, ya ce har kullum gwamnatin kasar Sin na maraba da kamfanoni daga ko ina a duniya, da su zuba jari tare da bunkasa kasar. He ya ce kasar Sin na yin taka tsantsan wajen tafiyar da batun sassa da take sanyawa cikin jerin wadanda ba za a iya dogaro da su ba, tana kuma daukar matakin ne kadai kan sassa waje kalilan, dake zama barazana ga tsaron kasar.

Jami’in ya kara da cewa, Sin ta sha alwashin bin turbar samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fitar da mafi kankantar iskar carbon mai dumama yanayi, da gabatar da shawarwari na shawo kan kalubalen dake addabar duniya.  (Saminu Alhassan)