logo

HAUSA

Sin: Ziyarar da shugaban Equatorial Guinea zai gudanar a Sin za ta raya huldar sassan biyu

2024-05-23 19:20:05 CMG Hausa

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin zaman ya ambaci ziyarar da shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo zai gudanar a kasar Sin.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, an yi imani ziyarar da shugaba Mbasogo zai gudanar za ta ingiza kuzarin ci gaban dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu, kana za ta inganta hadin gwiwar sassan biyu a fannoni daban daban, ta yadda za su samu sabbin sakamako.

Game da atisayen da rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar take gudanarwa a mashigin tekun Taiwan kuwa, Wang Wenbin ya ce atisayen hukunci ne ga ayyukan ‘yan aware na yankin Taiwan, kuma gargadi mai tsanani ga masu tsoma baki daga sassan waje.

Game da maganganun da suka shafi yankin Taiwan, da wasu jami’an kasar Japan suka furta kuwa, Wang Wenbin ya ce, batun yankin Taiwan jigo ne cikin muhimman moriyar kasar Sin, kuma jan-layi wanda ba za a tsallaka shi ba. Bangaren Sin ya bukaci bangaren Japan, da ya cika alkawarin tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya ta hanyar da ta dace.

Game da taron shugabannin Sin da Japan, da Koriya ta Kudu, wanda za a gudanar nan ba da jimawa ba, Wang Wenbin ya bayyana cewa, bangaren Sin na fatan inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali, da wadata a shiyyar da kuma duk duniya baki daya tare da bangarorin Japan, da Koriya ta Kudu. (Safiyah Ma)