Lai Ching-te ya kafa tarihin kunyata a idon duniya
2024-05-23 15:32:14 CMG Hausa
Tsakanin ranekun 23 zuwa 24 ga watan nan da muke ciki, rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar ta shirya sojojin kasa, da na ruwa, da na sama, da na rokoki da sauransu, don yin atisayen soja na hadin gwiwa, mai taken “Joint Sword-2024A”, a kewayen tsibirin Taiwan. Hakan wani mataki ne da kasar Sin ta dauka, don kare mulkin kanta da cikakkun yankunanta, kuma martani ne ga ayyukan ‘yan aware na yankin Taiwan, kana kashedi ne da Sin ta yi wa kasashen da suka tsoma baki cikin batun yankin Taiwan.
Jawabin da jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar a ranar 20 ga watan nan, ya bayyana aniyarsa ta raba yankin Taiwa daga kasar Sin, lamarin da ya keta hurumin manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, yayin da ya bata yanayin zaman karko a yankin. Shi ya sa, ya zama wajibi gwamnatin kasar Sin ta mayar da martani, kuma ko shakka babu martanin ya kasance halastacce ne. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)