logo

HAUSA

CMG ya kaddamar da kasaitaccen bikin AI

2024-05-23 14:17:43 CMG Hausa

 

Babban rukunin gidan rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG, da ofishin kula da harkokin Intanet da sadarwa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatin lardin Guangdong na kasar, sun yi hadin gwiwar kaddamar da kasaitaccen biki game da fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adama ko AI na shekarar 2024, a birnin Shenzhen na lardin na Guangdong. Shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci bikin da ya gudana a jiya Laraba.

Yayin bikin, an gabatar da takardar bayani kan bunkasuwar fasahar AI da CMG ya samu. Kuma CMG ya gabatar da ka’idoji hudu na amfani da fasahar AI, wato kokarin nazari da gaggauta amfani da fasahar, da nacewa ga manufofin aiwatarwa bisa ka’idojin da aka tanada, kana da samun ingantaccen ci gaba bisa kimiyya, har ma da bude kofa da yin hadin gwiwar cin moriyar juna, tare da tsara matakan da za a dauka wajen amfani da fasahar AI a bangaren samar da shiriye-shirye, da ba da jagoranci ga aikin kirkire-kirkiren kafofin yada labarai, da ma yi wa tsarin kafofin kwaskwarima, da zummar nuna hanyar da za a bi wajen ingiza bunkasuwar AI yadda ya kamata. (Amina Xu)