logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Rizhao dake lardin Shandong

2024-05-23 14:54:07 CMG Hausa

 

Da yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai rangadin aiki a birnin Rizhao dake lardin Shandong, inda ya ziyarci tashar jiragen ruwa ta Rizhao, da hanyar zirga zirgar mutane ta zirin gabar teku.

Shugaba Xi ya fahimci yadda ake gaggauta raya tashar ba tare da bata muhalli ba kuma bisa fasahohin zamani, da ma yadda birnin ke kara bude kofarta ga ketare, da karfafa kiyaye muhallin gabar tekun, kana da kyautata zaman rayuwar jama’a da sauransu. (Amina Xu)