logo

HAUSA

Xi jinping ya taya murnar bude taron dandalin hadin gwiwar sin da kasashen GCC kan masana’antu da zuba jari

2024-05-23 14:47:53 CMG Hausa

 

Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da wasikar taya murnar bude taron dandalin hadin gwiwar Sin da kwamitin hadin kan kasashen Larabawa na yankin Gulf, wato GCC kan masana’antu da zuba jari.

Cikin sakon nasa Xi Jinping ya nuna cewa, Sin da kasashen GCC, na da dadadden zumunci har na tsawon fiye da shekaru dubu. A shekarar 2022, an cimma nasarar gudanar da taron koli karo na farko a tsakaninsu, matakin da ya bude sabon babin zurfafa hadin gwiwarsu. Ya ce habaka hadin kan bangarorin biyu, a fannin raya masana’antu da zuba jari, zai kawo zarafi mai yakini na inganta aikin hada shawarar “ziri daya da hanya”, da tsare-tsare da muradun raya kasashen GCC baki daya, ta yadda za su amfani juna da cin gajiyar fifikon juna, da ma raya sabon karfin bunkasuwa, da tabbatar da samun ci gaban juna.

A wannan rana, an bude wannan dandali, wanda kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin, da gwamnatin lardin Fujian suka yi hadin gwiwar shiryawa a birnin Xiamen na lardin. (Amina Xu)