logo

HAUSA

Kuri’un jin ra’ayi na CGTN sun nuna kin amincewa da kalamai masu matukar hadari na jagoran Taiwan

2024-05-22 20:58:50 CMG Hausa

A ranar Litinin 20 ga watan nan, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin ya yayata manufar “’Yancin Taiwan”, lamarin da ya yi matukar jan hankalin sassan kasa da kasa.

Wata kuri’ar jin ra’ayin al’ummun kasa da kasa, da kafar watsa labarai ta kasar Sin ta CGTN ta gudanar, ta nuna cewa, kusan kaso 90 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin su, na matukar goyon bayan manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, sun kuma nuna adawa da manufar neman “’Yancin Taiwan” ta ‘yan aware.

Wannan kuri’a da CGTN ta wallafa a dandalolin harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci da harshen Rasha, ta samu masu bayyana ra’ayoyi har mutane 11,645 cikin sa’o’i 24.  (Saminu Alhassan)