logo

HAUSA

Xi ya taya murnar bude tattaunawar manyan jami’an Sin da Amurka a fannin yawon shakatawa karo na 14

2024-05-22 14:49:14 CMG Hausa

 

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar kaddamar da tattaunawa tsakanin manyan jami’an Sin da Amurka a fannin yawon shakatawa karo na 14.

Cikin sakon nasa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana ake cika shekaru 45, da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka. Al’ummomin kasashen biyu tushe ne na huldarsu, wadanda kuma suka bude kofar huldar kasashen, da ma rubuta labaran sada zumunta tsakaninsu, kuma makomar huldar kasashen biyu na dogaro da su.

Xi Jinping, ya kuma nanata fatansa ga bangarori daban daban, da su kara mu’amala, da cimma daidaito, da daukar matakan da suka dace, su kuma inganta yin mu’amala ta hanyar yin hadin gwiwar sha’anin yawon shakatawa, su bunkasa zumunci ta hanyar yin mu’amalar al’adu, a kokarin aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a San Francisco. (Amina Xu)