logo

HAUSA

Sabon tsarin kasuwanci ya raya kasuwannin furanni na Kunming

2024-05-22 16:46:33 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barka da war haka. Kwanan baya, kasuwar furanni ta Dounan dake birnin Kunming, na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta sayar da furanni da yawa. A wannan kasuwa, furannin dake da sunaye masu alamta samun sa’a, da tsarin yin odar furanni ta intanet, sa’an nan a kai furannin zuwa gida, sun samu karbuwa matuka daga wajen masu sayayya.