logo

HAUSA

Sin na bukatar wasu kasashe da 'yan siyasa su daina siyasantar da batutuwan da suka shafi yankin Taiwan

2024-05-21 21:02:20 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kin amincewa da yin mu’ammala a hukumance tsakanin kasashen dake da huldar diplomasiyya da Sin da yankin Taiwan.  

Wang Wenbin ya bayyana haka ne yau Talata, yayin taron manema labarai na yau da kullum, inda wasu ‘yan jarida suka nemi jin ra’ayin kasar Sin game da yadda wasu 'yan majalisar dokoki da tsoffin ‘yan siyasa daga kasashen dake da huldar diflomasiyya da kasar Sin, suka halarci bikin rantsar da wanda ake kira "shugaban yankin Taiwan" Lai Ching-te, kuma suka taya shi murna. 

Kakakin ya kara da cewa, maganganu da ayyuka marasa dacewa da wasu kasashe da ‘yan siyasa suka yi dangane da batun, sun keta manufar kasar Sin daya tak da manyan ka’idojin dangantakar kasa da kasa. Haka kuma tsoma baki ne cikin harkokin siyasar cikin gidan Sin, kuma ya gurgunta ikon mulkin Sin da mallakar cikakkun yankunanta, lamarin da Sin din ke Allah wadai da shi matuka.

Game da "taya murna" da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi wa wanda ake kira da shugaban yankin Taiwan game da bikin rantsar da shi, Wang Wenbin ya ce, matakin da Amurka ta dauka ya keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma sanarwoyin hadin gwiwa uku da Sin da Amurka suka fitar. Yana mai cewa, ba za a iya girgiza tsarin kasa da kasa na bin manufar kasar Sin daya tak ba.

Har ila yau, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ba da shawarar daukar matakan da suka dace kan Michael Gallagher, tsohon dan majalisar dokokin Amurka dake yawan tsoma baki cikin harkokin siyasar cikin gidanta.

Ban da wannan, Wang Wenbin ya tabo dokar da Amurka ke kira "Dokar hana aikin tilas ga 'yan kabilar Uygur", inda ya ce, ba ta kare hakkin bil'adama. Maimakon hakan, tana fakewa karkashin tutar hakokkin dan Adam, tana keta hakkin rayuwa, da ayyukan yi, da ci gaban jama'ar jihar Xinjiang. Ya ce kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don kiyaye hakkoki da moriyar kamfanoninta. 

Dangane da batun mika Julian Paul Assange, wanda ya kafa shafin "WikiLeaks", Wang Wenbin ya ce, lamarin ya nuna cewa,"’yancin watsa labarai" kamar abin da ake kira "dimokradiyya" da "’yancin bil’adama," ba komai ba ne illa wani makami da Amurka ke amfani da shi don murkushe 'yan adawa da kuma kiyaye ikon mulkinta.

Dangane da rikicin Falasdinu da Isra'ila kuwa, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin tana goyon bayan duk kokarin da kasashen duniya suke yi na sa kaimi ga warware batun cikin adalci da samar da mafita mai dorewa, kana tana goyon bayan kasashen Larabawa da su karfafa hadin kai, da kuma taka rawar gani kan batun.

Har ila yau yayin taron manema labaran na yau, Wang Wenbin ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa mu'amala da hadin gwiwa da bangaren Amurka a fannin fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama. (Safiyah Ma)