logo

HAUSA

Manyan jami’an Malaysia da Cambodia da Brazil za su ziyarci Sin

2024-05-21 21:03:02 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya sanar yau Talata cewa, mataimakin firayin minista na farko kuma ministan raya kauyuka da yankuna na Malaysia, Ahmad Zahid Hamidi, zai ziyarci Sin daga ranar 22 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni.

Haka kuma, mataimakin firaminista kuma ministan kula da harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Cambodia, Sok Chenda Sophea, zai ziyarci Sin daga ranar 23 zuwa ranar 25 ga watan Mayu.

Haka zalika, babban mashawarci na musamman na shugaban Brazil, Celso Amorim, zai ziyarci Sin daga ranar 22 zuwa ranar 29 ga watan Mayu. (Safiyah Ma)