Sin da Afrika ta Kudu sun amince da bunkasa dangantakar soji a tsakaninsu
2024-05-20 20:20:12 CMG Hausa
Ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya gana a yau Litinin da shugaban rundunar sojin ruwan Afrika ta Kudu Monde Lobese a birnin Beijing, inda suka amince da bunkasa dangantakar soji dake tsakanin kasashen biyu.
A cewar Dong Jun, rundunonin sojin kasashen biyu na musaya sosai, kana hadin gwiwar rundunoninsu na ruwa ya kasance a kan gaba. Ya ce bangarorin biyu sun amince da karfafa tuntubar juna da zurfafa hadin gwiwa da hada hannu wajen tunkarar kalubale da barazana.
A nasa bangare, Monde Lobese, ya ce hadin gwiwar sojin ruwa tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da yin zurfi a shekarun baya-bayan nan, kuma a shirye Afrika ta Kudu take ta hada hannu da Sin wajen ingiza dangantakarsu a fannin aikin soji, zuwa wani sabon mataki. (Fa’iza Mustapha)