logo

HAUSA

An dakile wani yunkurin juyin mulki a Kinshasa

2024-05-19 20:29:38 CMG Hausa

Rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta ce an dakile wani yunkurin juyin mulki a Kinshasa, babban birnin kasar, a yau Lahadi.

Kakakin rundunar Sylvain Ekenge, ya bayyana yayin wata sanarwa da aka gabatar ta kafar talabijin cewa, rundunar na tabbatar da cewa an shawo kan yanayin, kuma tana kira ga jama’a su ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba. Ya kara da cewa, an cafke da dama daga cikin wadanda suka shirya juyin mulkin.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa, an samu asarar rayuka akalla 3 yayin da maharan suka yi yunkurin kutsawa unguwar da ‘yan siyasa da jami’an diflomasiyya suke zama a birnin Kinshasa da safiyar yau. (Fa’iza Mustapha)