logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya gana da shugabannin babban kamfanin gina layikan dogo na kasar Sin CRCC

2024-05-19 14:54:38 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa shugabannin babban kamfanin gina titunan jiragen kasa na Sin CRCC cewa kada su nuna fargaba wajen zuba jarin su a Najeriya kasancewar yanzu an samu kwanciyar hankalin da ya kamata a kowanne sashen na kasar.

Shugaban ya tabbatar da hakan ne ranar juma`a 17 ga wata a fadar sa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kamfanin gine-ginen layikan dogo na kasar Sin CRCC Mr. Dai Hegen, ya basu tabbacin kare dukkannin jarukan da suka saka a Najeriya sannan kuma gwamnati za ta kara karfafa alakar kasuwanci da kamfanin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya cigaba dacewa gwamnatin sa tana marhabin dukkan damarmakin fadada harkokin kasuwanci da kamfanin, yace bisa yadda ya lura tsarin ayyukan kamfanin na CRCC ya dace da manufofin gwamnatin Najeriya wajen sake fasalta tsare-tsaren cigaban tattalin arzikin kasa, wanda dukkannin bangarorin biyu za su ci gajiya.

Yace hakika Najeriya ta ga fa`idar aiki tare da kamfanin a fannoni daban daban musamman sha`anin gina layikan dogo.

Alhaji Sa`idu Alkali shi ne ministan sufurin na tarayyar Najeriya ya yi wa manema labarai Karin haske a game da taron jim kadan da fitowar su.

“Kamfanin CRCC shi ne jagora na wasu daga cikin kamfanonin kasar China a Najeriya wadanda suke gudanar da aiyuka daban daban a ma`aikatar aiyuka da ta sufuri da kuma ma`akatar lura da sufurin jiragen sama da sauran bangarorin cigaban tattalin arziki, kuma shugaban kasa ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa wajen hada kai da kasar China domin gina Najeriya”

Ministan kudi na tarayyar Najeriya Mr. Wale Edun ya kasance shi ma a wajen taron.

“ Mun tattauna akan yadda za a samar da kudden tafiyar da ayyuka, mun kuma tattauna akan ayyukan da ake kan gudanar da su yanzu haka, babban abun farin cikin shi ne baya ga gudanar da ayyukan kamfanin na CRCC zai kuma rinka bada taimakon kudade wajen gudanar da ayyuka”.(Garba Abdullahi Bagwai)