logo

HAUSA

Firaministan Sin ya gana da tawagar CBBC daga Birtaniya

2024-05-18 16:25:43 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da tawagar kungiyar ‘yan kasuwar Sin da Birtaniya ta CBBC, karkashin jagorancin shugabanta Sherard Cowper-Coles.

Yayin zantawarsa da tawagar ‘yan kasuwar, Li Qiang ya ce, Sin za ta kara fadada damar shiga kasuwanninta, da karfafa tabbacin hidimomi ga  masu zuba jari daga ketare. Ya ce, Sin a shirye take ta kara azamar bunkasa musayar tattalin arziki da cinikayya da Birtaniya, da raba damammakin samar da ci gaba, da fadada hadin gwiwa a fannonin hada-hadar kudi, da sabbin makamashi, da likitancin zamani, da tattalin arzikin dijital da sauran sassa, kana tana ingiza hadin gwiwar karin sassa, karkashin manufofin da aka tsara karkashin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya.

A nasa bangare kuwa, mista Cowper-Coles cewa ya yi, kungiyar CBBC na goyon bayan Sin, bisa manufarta ta yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, da burin samar da ci gaba mai inganci. Kaza lika, kungiyar ta sha alwashin ci gaba da zama gadar hade sassan biyu, da ba da kyakkyawar gudummawar bunkasa ci gaban alakar Birtaniya da Sin, da zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu.  (Saminu Alhassan)