logo

HAUSA

Gidajen adana kayan tarihi na Sin sun karbi masu ziyara biliyan 1.29 a shekarar 2023

2024-05-18 15:56:48 CMG Hausa

Hukumar lura da kayayyakin gadon al’adun gargajiya ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2023, gidajen adana kayan tarihi na kasar sun karbi baki masu ziyara da yawansu ya kai biliyan 1.29, adadin da ya dara na shekarar 2022.

Hukumar ta bayyana alkaluman ne a Asabar din nan, yayin bikin ranar gidajen adana kayan tarihi ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin.

A cewar hukumar, a shekarar ta bara, gidajen adana kayan tarihi dake sassan kasar Sin sun gudanar da nune-nune sama da 40,000, da ayyukan ilmantarwa sama da 380,000.

Har ila yau a dai shekarar ta 2023, an yi rajistar sabbin irin wadannan gidaje har 268 a sassan kasar Sin, wanda hakan ya kai jimillarsu zuwa 6,833. A daya bangaren kuma, kasar Sin na kara fadada aiwatar da manufar baiwa al’umma damar ziyartar gidajen adana kayan tarihin kyauta, inda kawo yanzu sama da kaso 90 bisa dari na gidajen ana ziyartar su ne kyauta.   (Saminu Alhassan)